Hausa language is one of the most predominant languages in Northern Nigeria, and Hausa Proverbs are used in everyday conversation around the North and even beyond.
So we decided to bring you Great Hausa proverbs from our collection. please enjoy and dont forget to submit yours in the comment section below.
Abin aljihu, na mai riga ne.
A yi wadda za a yi! Bera ya zubda garin kyanwa
Abin al’ajabi! Ango ya kwana da kunzugu
Abin Allah! Budurwa da jika
Abin Allah, na Annabi ne
Duk wanda ya kona rumbunsa, ai shi yasan inda toka ke tsada
Haihuwa fari horon Gaba
Rashin sani yafi dare duhu
Hatsi yayi banza su kaza harda bakace
Ta faru ta kare anyi wa mai dame daya sata.
Kowa yaci ladan kuturu dole yayi masa aski
Banza batakai zomo kasuwa
Nashiga ban daukaba bata fidda barawo
A rashin sani, bako ya sha ruwan wanka
A rika sara, ana duban bakin gatari
A sa a baka, ya fi a rataya
A san mutum, a san cinikinsa
A sayar a fadi, karin wayo
A so kare, har jelarsa
Bishiya daya bata daji
Rabon kwado Ko yahau sama sai ya sauko
Abin aro, ba ya ado
Ba a nuna sani a kasuwar jahilai
Durqusa ma wada ba gajiyawa ba ne.
Idan yaro yace zai yi huda sakammar garma.
Hanu daya baya daukan jinka.
Mai uwa a gindin murhu, ba ya cin tuwonsa gaya.
Aikin banza harara a duhu
Gyara kayan ka bai zama sauke mu raba ba.
Komai nisan Jifa kasa xai fado
sabon shiga barawo da sallama
Wanda ya raina tsayuwar wata ya hau ya gyara
Na gaji da gafara Sa ni banga kaho ba
Dan kuka ke ja ma uwarshi jifa
Ta Yaro Kyau Take Bata Karko
Abun dariya wae yaro yaga haqori
Da ba’a san asalin angulu ba da tace daga misra tazo
Tun kafun a haifi uwar mai sabulu balbela da farin ta
Ba anan take bah wai an danne bodari ta kaa
Wadata shuka da bakin buhu
Wai ana biki a gidan su kare yace mugani a kasa
Rikicin duniya da mai rai akeyi
Idan angulu ta bia maka maradi, zabua ta taffi da zanenta.
Kaga rabo, auren mace da ciki
Inda rabon kura a takobi, Sai a Saida takobi a siya akuya, kuran ta cinye akuyar.
Idan bera da sata toh daddawa ma na da wari
Idan kaga kemun dan’uwanka ya kama da wuta, toh shafa wa taka ruwa.
Karamin kuturu shi ya ke yin ‘Allazi Wahidun’, babba kuwa sai da ‘Ya Wahhabu’
Hassada ga mai rabo taki
Ba’a hada gudu da susar duwawu
Komai girman gona akwai kunyan karshe
Baza ta sabu ba, wankan kuturu da sabulu
Kifi tana kallonka me jar koma
Neman gurin zama, gaishe da uwar saurayi a kasuwa
Ba haka aka so ba, qanin miji yafi miji kyau
Duk tsadar atamfa watarana sai an daure kafar kaza da ita.
Kowa ya tuba dan wuya ba lada
Kowa yaci bashin kura baya maraice daji
ko anci goro an sha bauri
Maganin a dena kar Afara
Gaba da gabanta wai aljani ya taka wuta
Abun da Kamar wuya. Wae gurguwa da auren nesa
Kwarya tabi kwarya in tabi akushi rugurgujewa zatayi
Akwana a tashi jariri zai zama ango
Alamar kiba tana ga mai jiki
Mai ci da uwa ba shi kuka’n sudi.
Da ruwan ciki akejan na rijiya
Wanda ya isa ya kai shi Ke saida ruwa a bakin rafi.
Sandan dake hannunka da ita ake kai duka
Ikon Allah wai na kwanche ya fadi
Ma hakurci mawa daci
Mai hakuri yakan dafa dutse har yasha romonsa
Da kadan da kadan matankadi kan shiga gora
Wanda baiyi sharan masallaci ba zai yi ta kasuwa
Daga ganin Sarki Pawa Sai Miya tayi Zaki
Sawun giwa ya taka na rakumi
Duk dan da yace maman shi baza ta huta bah. Shima ba zai huta bah
Inda Amana wuta bazataci makeri baa
Aikin banza harara a duhu
Sabo da kaza baya hana yanka.
Allurar cikin ruwa Mai Rabo ka dauka
Ganin buzu a masallaci ya ishe rago wa’azi
Ciki da gaskiya wuka bata hudashi.
Dan hakkin da ka rena shi kan tsoni maka ido
Shure shure bai hana mutuwa
Barewa ba za tayi gudu ba, dan ta yayi rarrafe
Bakin rijiya ba wajen wasan makaho ko yaro bane.
Zama da madaukin kanwa shi yake kawo farin kai
Kowa da kiwon da ya karbeshi wai makwamcin mai akuya ya siya kura
Hannun daya qirga riba wataran zai qirga faduwa1
Labarin zuciya ka tambayi fuska
Duk inda shanuwar gaba tassha ruwa sena baya itama ta bita
Zara bata barin dame
Ba a boye chibi ranan wanka
“Me ya rage wai?” ance da kuturu Allah ya la’ance kah.
Da mugun rawa, gwamma qin tashi.
Kowa da kiwon da ya karbe shi, makwabcin me akuya ya siyo kura
Idan kura na maganin zawo tayiwa kanta
Click the link to read from our collection of Funny Hausa Proverbs