The Largest Collection of Hausa Proverbs (Karin Magana) On The Net

1000 Hausa Proverbs (Karin Magana)

Written by Editorial Staff

Editorial Staff is a team of Editors and Authors Trusted by over 1.3 million readers worldwide.

March 2, 2021

Hausa Language is one of the most common and widely spoken languages in Africa and indeed the world. Spoken by over 80 million people globally, the Language is one of the most popular languages in the world. Proverbs, along with ‘kirari’ (epithets), habaici, tatsuniya (folklore) represent some of the ways native speakers express themselves in the Language.

Just like English proverbs, parables, and idioms, Hausa proverbs, called Karin Magana are vital in the development of the language and the Hausa culture. Karin Magana are mostly short, witty, and hilarious and is communicated orally. This perhaps explains the lack of Karin Magana on the internet, as most of them were lost. With over one thousand (1000) Karin magana, this is the largest collection of Hausa Proverbs on the internet. Do enjoy, and don’t forget to share.

List Of 1200 Hausa Proverbs (Karin Magana)

A

 1. A bakin tsoho goro kan tsufa
 2. A bakin wawa ake jin Magana
 3. A bari ya huce shi ke kawo rabon wani
 4. A bar kaza cikin gashinta
 5. Abin ba dadi, mahaukaci ya tauna kasha
 6. Abin bai dace ba, an ga Malami da gatari
 7. Abinda babba ya gani a zaune, yaro ko ya hau rimi ba zai gan shi ba
 8. Abinda ruwan zafi ya dafa, in an hakura, ruwan sanyi ma saiya dafa
 9. Abinda ya bata a duniya in an je lahira a ganshi
 10. Abin da ya kori bera ya fada wuta, yafi wutar zafi
 11. Abin da sake, an bai wa mai kaza kai
 12. Abin da sake an bai wa mai rogo bawo
 13. Abin da yawa, mutuwa ta je kasuwa
 14. Abin da Allah Yayi, Annabi sai ceto
 15. Abinda sauki, mutuwar bako a gari
 16. Abin da ka gani a gidan Kaura yana na Goje
 17. Abin da zuciya ya dauka, gangan jiki ma dole ya dauka
 18. Abin da baki ya daura, hannu bay a kwancewa
 19. Abin mamaki, mai karfi na bara
 20. Abin mamaki furar sayarwa a akushi
 21. Abin mamaki kare da tallan tsire
 22. Abin mamaki mai gari gwauro talaka da mata hudu
 23. Abin mamaki bay a karewa, rakumi ya shiga kuratandu
 24. Abin mamaki matar falke ta haifi jaki
 25. Abin nema ya samu, matar dan doka ta haifi barawo
 26. Abin nema ya samu, matar falke ta haifi jaki
 27. Abokin kirki ya fi mugun Dan uwa
 28. Abokin cin mushe ba’a boye mashi wuka
 29. Abin mamaki baya karewa, rakumi ya shiga kuratandu
 30. Abin nema ya samu, matar dan sanda ta haifi barawo
 31. Abin ya girma, kashe kwarkwata da tabarya
 32. Abin rabo ne, kuturu ya kama tarwada
 33. Abin fada na mai baki ne
 34. Abu a rufe mai raba zumunci
 35. Abu kamar wasa, karamar Magana ta zama babba
 36. Abu uku su ne maganin zaman duniya, tawakkali, dangana da hakuri
 37. Abu namu maganin a kwabe mu
 38. A bugi juji domin a ji karar gwazarma
 39. Abokin kirki ya fi mugun dan uwa
 40.   Abokin sarki, sarki ne
 41. Abokin kuka ake gaya wa mutuwa
 42. A ci baa sayar ba, kwai ya fi doki
 43. A ci a rage, shi ne ci
 44. A cikin ido ake tsawurya
 45. A daga sama an yi wa wada sata
 46. A dafa a daka a tankade sai kalwa
 47.  A dade ana yi sai gaskiya
 48. Adinga zuwa rafi wata rana a fasa tulu
 49. A duke ka a hana ka kuka
 50. Addu’a maganin annoba
 51. A dubi ruwa a dubi tsaki
 52. A jamu akai an ba uwar makaho kasha
 53. A jefar da kwallon mangwaro a huta da kuda
 54. A gayawa wani riginginin farin wata, agola kafi masu gida
 55. A aiki kare ya aiki wutsiya
 56. Aiki da hankali yafi aiki da agogo
 57. Aikin bakon raggo, raggo bakon aiki
 58. Aikin banza hutun jaki da kaya
 59. Aikin banza jefa agwagwa a ruwa
 60. Aikin banza zani da aljuhu
 61. Aikin banza bille a ciki
 62. Aikin banza talaka ya grime sarki
 63. Aikin banza yin kiba a kunne
 64. Aikin banza kiwon makahon kare
 65.  Aikin banza kare da gudun laya
 66.  Aikin banza sauri ba wurin zuwa
 67. Aikin banza makaho da waiwaye
 68. Aikin banza harara a duhu
 69. Akuya ko bata haihuwa tafi kare
 70. Akuya tayi wayo da yankakken kunne
 71. A kan wanke tukunya domin tuwan gobe
 72. Allah ke gyara tuwon makauniya har a ci ba kuda ba gashi
 73. Allah ke ci da maraya ko da mai uba bai so ba
 74. Allah suture bukwi in ji kishiyar mai doro
 75. Allah gatan kowa
 76. Allah na taimokon wanda ya taimaki kanshi
 77. Allah shi ke baiwa maraya ko da mai uwa bai so ba
 78. Allah Ya ci da na gari ba mugu ba
 79. Allah Yayi aure da mara kwabo
 80. Allah Ya gyara rimi cediya ta daina fushi
 81. Allah Ya wadarai naka ya lalace rakumin dawa yaga na gida
 82. Allah Ya kai yaro matsiyin babba
 83. Allah Ya bamu lafiya baba yaga tsirara
 84. Allah Ya kai damo ga harawa ko bai ci ba yayi birgima
 85. Allah Ya ba na zaune albarkacin na tsaye
 86. Allah Ya tsare gatari ga noma
 87. Allah Ya hada mu da mai son mu koda mugune
 88. Allah Ya fishemu da hawa dokin zuciya
 89. Allah Ya ba mai rabo sa’a
 90.  Allah Ya hana kunya ranar gaskiya
 91.  Allah Ya kawo kudi talauci ya ji kunya
 92. Allura a cikin ruwa mai hikima kan tsinta
 93. Allaura a cikin teku mai daukanta sai mai dace
 94. Alkawari kayane in a dauka sai an cika
 95. Alamar rago tana ga daurin bante
 96. Alamar karfi tana ga mai kiba
 97. Albarcin kaza kadangare ke shan ruwan kasko
 98. Albasa bata yi halin ruwa ba
 99. Alheri gadon bacci ne
 100. Alheri dan dankone ba ya faduwa kasa banza
 101. Alheri ne bakon gishiri a shekara ana lashewa
 102. Alhaki kuykuyo ne mai shi yake bi
 103. Almajiri tsutsune in ya ci sai ya tashi
 104. Amfanin abun ado daurawa
 105. Amfanin sani aiki da shi
 106. Amarya bata laifi koda ta zagi ‘yar masu gida
 107. An bar kyau tun ranar haihuwa
 108. An bar jaki ana dukan taiki
 109. Anci moriyar gangan an jefar da kware
 110. An dade ana gafara ga sa ba’a ga kaho ba
 111. An daga sama anyi wa wada sata
 112. An ki cin biri an ci dilla
 113. An raba hankali na biyu ance ya sha fura a je gona
 114. An rabu ba kare bin damo
 115. An sha kanwa kwarnafi ya kwanta
 116. Ana barin halas dan kunya
 117. Ana babbakar giwa wa ke ta zomo?
 118. Ana bikin duniya ake na kiyama
 119. Ana dariya mai tauna kan koshi
 120. Ana fakewa da guzuma ana harbin karsana
 121. Ana ganin wuyan biri ake daureshi a kwankwaso
 122. Ana gudun gara an fada zago
 123. Ana rabaka da kiwon akuya kana kyalla ta haihu
 124. Ana rabaka da kaya kana nade gammo
 125. Ana sara ana duban bakin gatari
 126. Ana son wawa, haihuwarsa ne ba’a so
 127. Ana yabon ka sallah, ka kasa alwala
 128. Ana yi da kai yafi ba’a yi, sarki ya koma mai anguwa
 129. Ana zaton wuta a makera, sai gashi a masaka
 130. Annurin fuska kaurin hanji
 131. An gara jakan mafaurata
 132. Aci ba’a sayar ba kwai yafi doki
 133. A cikin ido ake tsawurya
 134. Anyi asarar kanwa tunda wake ya lalace
 135. Anyi ba’a yi ba ba ance tsirkiyada fatan kunkuru
 136. A ramawa kura aniyarta
 137. Arha cefane kunu daga ruwa sai tsamiya
 138. Arha kamar jamfa a jos
 139. Arha maganin mai wayo
 140. Arha wanzami ya samu kan mai saiko
 141. A rashin kira Karen bebe ya bata
 142. A rashin farin wata tauraro ke haske
 143. A rashin sani kaza ta kwana kan dami
 144. A rashin sani bako ya sha ruwan wanka
 145. A rashin tayi akan bar arha
 146. A rashin tuwo akan ci wake a kwana
 147. A rashin uwa ake uwar daki
 148. A ruwa ake dadewa ba a wuta ba
 149. Arziki rigar kaya kana ja yana ja
 150. Arziki rigar kaya ga dadi ga suka
 151. An sha ruwan gwangwala a kara tsayi
 152. A sa a baka ya fi a rataya
 153. Asalin birni kauye ne
 154. A tambayi me kundumi labarin kitse
 155. A taru a kashe mahaukacin kare
 156. Ayi wanda za’a yi bera ya zubar da garin kyanwa
 157. Ayi a hankali kada a sha ruwa da haki
 158. Ajiya maganin wata rana
 159. A kwana a tashi jariri ango ne
 160. A kwana a tashi yaro tsoho ne
 161. Akwai ranar kin dillaci randa rigar mai gari ta bata
 162. “A yi abunda za’a yi” ramamme ya zagi maye

B

 1. Ba sauran waka, an yanke harshen zabiya
 2. “Ba samun duniya ba” wurin da za’a zauna a ji shine injin dan tsako
 3. Ba’a bari, a kwashe duka
 4. Ba’a fasa randar daki ba’a shigar da na waje ba
 5. Ba’a fafe gora ranar tafiya
 6. Ba’a fushi da yin Allah
 7. Ba’a gane kyaun gini sai anyi yabe
 8. Ba’a gaggawar fara’a
 9. Ba’a jan ragama da rigima
 10. Ba’a kada miya tun dawa na rumbu
 11. Ba’a kin ta mutane ance bazawara ta koma gidan mijinta
 12. Ba’a kin mutane ance barawo yayi gudu
 13. Ba’a koyan karatu ran tukuri
 14. Ba’a sarki biyu a gari daya
 15. Ba’a shan zuma sai an sha harbi
 16. Ba’a shan zuma sai da wuta
 17. Ba’a sayan jaki don a ci sai don daukan kaya
 18. Ba’a san maci tuwo ba sai miya ta kare
 19. Ba’a sake wa tuwo suna
 20. Ba’a shiga sharo ba shanu
 21. Ba’a raba hanta da jini
 22. Ba’a riga malam masallaci
 23. Ba’a raina zakin gwandan daci don ba’a bata ruwa
 24. Ba’a hada gudu da susan duwawu
 25. Ba’a hada gudu da susan katare
 26. Ba’a hana mabada rago fata
 27. Ba’a karbe wa yaro garma
 28. Ba’a maida hannun kyauta baya
 29. Ba’a mugun sarki sai mugun bafade
 30. Ba’a nunawa kurciya baka
 31. Ba’a saurin yabon dan kuturu sai ya girma yatsun sa
 32. Ba’a wasan wuta a gidan kara
 33. Ba’a wuce makadi da rawa
 34. Ba’a yi wa biri burtu
 35. Ba’a yin nitso a masaki
 36. Ba’a yanka karfe sai da karfe
 37. Ba bako ruwa ka sha labara
 38. Baka cin zamanin ka ka ci na wani
 39. Ba cinya ba kafar baya
 40. Ba dan tsayi akan ga wata ba
 41. Ba domin tuwo akayi ciki ba
 42. Ba dukan ruwan sama ke da wuya ba , ruwan ganye
 43. Ba fada da malam ba, asari ake tsoro
 44. Ba gagararre sai bararre
 45. Ba iya kwanciya aka fi kare ba sai dai abun rufa
 46. Baka do gadon mutun amma kana da gadon batun sa
 47. Ba ji ba gani auren kurma da makaho
 48. Ba maraya sai rago
 49. Ba mai yi sai Allah
 50. Bani na kashe zomon ba rataya aka bani
 51. Ba shiga ba fita an ba mahaukaciya tsaron kofa
 52. Babban goro sai magogin karfe
 53. Babban kaya sai gammo
 54. Bako raba ne, yakan zo ya wuce
 55. Bako ba sallama wawa ne
 56. Bakon munafuki bana mutun daya bane
 57. Bakar inuwa gwamma ranar daki
 58. Bakin jinin mazuru mai kaza zagi, mara kaza zagi
 59. Bakin Karen masoyi yafi farin ragon makiyi
 60. Bakin tukunya mai fidda farin tuwo
 61. Bakin rijiya ba wajan wasan makaho bane
 62. Bakin da Allah Ya tsaga baya hanashi abinci
 63. Baki shi kan yanka wuya
 64. Balbela baki bin kare sai shanu
 65. Ban sa a ka ba in ji barawon taguwa
 66. Banga alama ba, ance wa kuturu ya gama lafiya
 67. Ba rabuwa da gwani ba, sai dai maida gwani kamar sa
 68. Bara nayi wake, bana nayi harawa
 69. Barawon rakumi daga daddawa ya fara
 70. Barewa baza ta yi gudu ba danta yayi rarrafe
 71. Bari neman jini ga babe, Allah bai yi shi da jini ba
 72. Bari murna Karen ka ya kama zaki
 73. Bashi hanji ne yana cikin kowa
 74. Ba’a yin rawa ba juyi
 75. Bayan wuya sai dadi
 76. Bayan ci zama sai gumi ne
 77. Ba kullun ake kwana a gado ba
 78. Ba kira mai ya ci gawayi?
 79. Ba mutuwan ake tsoro ba, sabo
 80. Ba wahalalle sai mai kwadayi
 81. Ba za’a ji mutuwar sarki a baki na ba
 82. Ba za’a ci kwado da yaro ba sai ya wanke hannunsa
 83. Baza ka ari bakina ba ka ci mun albasa ba
 84. Ba zama an saci dan barawo
 85. Banza a banza kare a karofi
 86. Banza girman mahaukaci, karami mai hankali ya fishi
 87. Banza bata kai zomo kasuwa
 88. Ban ci kasuwa ba, rumfa ba zai danne ni ba
 89. Barin kashi a ciki baya maganin yunwa
 90. Bikin faran kaza balbela ba gayya bace
 91. Bikin magaji baya hana na magajiya
 92. Bin na gaba bin Allah
 93. Biri da gatari a gona abin tsoro
 94. Bishiya mai ‘ya’ya ake jifa
 95. Biyan bukata yafi dogon buri


C

 1. Can ga su gada zomo yaji kiran farauta
 2. Can kake adon mai gona
 3. Ciki da gaskiya wuka bata huda shi
 4. Ciki mai manta kyautan jiya
 5. Cinikin duniya diban nono
 6. Cinnaka baki san na gida ba
 7. Cin wake na yara kumburin cikin manya
 8. Cin dadi ai sabo ne
 9. Cin danko harda su kaza
 10. Cin tuwon kishiya ramako
 11. Cin loma yafi jiran malmala
 12. Cin abinci dare daya kumburin ciki
 13. Ciwon da kare yayi idan dan akuya ne sai wuka
 14. Ciwon ‘ya mace sai ‘ya mace
 15. Ciwo ba mutuwa ba sai kwana ya kare
 16. Cin hakkin sama sai rakumi
 17. Ci naka in ci nawa, ba rowa bane halin zama ne
 18. Ci gaban mai ginin rijiya,yana zurfi ana shiga hatsari

D

 1. Da ba dan mun san asalin angulu ba, da nace daga masar take
 2. Da babu gwara ba dadi
 3. Dabara baya daura kaya sai igiya
 4. Da biyu an buge biri da rani
 5. Da biyu an bugi akuyar kishiya
 6. Da dan gari akan ci gari
 7. Da dama sarki a bisa jaki
 8. Da ganin kura kasan zata ci akuya
 9. Da ganin dan kunama zai yi harbi
 10. Daga ganin dutsen zuma, kasan daga dadi take
 11. Daga baya an yi sadaka da bazawara
 12. Da haka muka fara, kuturu yaga mai kyasbi
 13. Da itace mai kama ake kota
 14. Da kamar wuya a gasa kaza a yar
 15. Da kamar wuya gurguwa da auren nesa
 16. Da kukan zuci gwara na fili
 17. Da kyar na kai yafi da kyar aka kamani
 18. Da na gaba ake gane zurfin ruwa
 19. Da muguwar rawa, gwamma kin tashi
 20. Da sanin ango aka yi wa ‘yan buki duka
 21. Da sannu auduga zai zama zare
 22. Da sabon gini gwamma yade
 23. Da sabuwar rijiya gwamma yasa
 24. Da sauran tsalle an daura wa kwado garwashi
 25. Da sauran kuka an daurawa jaki kaya ba taiki
 26. Da tsirara gwara bakin bante
 27. Da tsohuwar zuma ake magani
 28. Da rarrafe yaro kan tashi
 29. Da ruwan ciki ake jan na rijiya
 30. Da rigimar ciki gwamma na waje
 31. Da uba ake ado ba da riga ba
 32. Da wuya ake gane fushin mai tsinin baki
 33. Da walakin goro a cikin miya
 34. Da wawanci gwara gidadanci
 35. Da wasa ake fada wawa Magana
 36. Da yayyafi kogi kan cika
 37. Da zafi zafi akan bugi karfe
 38. Dadi mai sa zabiya guda
 39. Dadin zama sai bare, wuyar zama sai dan uwa
 40. Dadin zama ke kawo bege
 41. Dadi na da gobe saurin zuwa
 42. Dadin duniya yana tsawo ana kara hallaka
 43. Dadewa a bauta ‘yanci ne
 44. Daidai ruwa daidai gari
 45. Daji ba’a sa mata kyaure
 46. Daki mai duhu, mara gaskiya ke tsoron shiga
 47. Dan adam mai wuyan gane hali
 48. Dan baiwa ‘yar albarka
 49. Dan banza yashi ne ko an dunkula shi baya dunkuluwa
 50. Dan hakin da ka raina shi ke tsole maka ido
 51. Dan kuka mai jawa uwarsa jifa
 52. Dan kuka baya zama dan tsamiya
 53. Dan jinjirin jimina gagara shaho dauka
 54. Dan jinjirin kura, kashe ki tausayi barinki takaici
 55. Dan tsako samo ki ki dangi
 56. Dan fari man gyada ne
 57. Dan kishiya rikon hakuri
 58. Dan uwa rabin jiki
 59. Dan masara ana goyon ka kana gemu
 60. Dami ya tsinke a gindin kargo
 61. Dama yaya lafiyar kura balle tayi hauka
 62. Daminan ta za tai kyau, daga bazara ake gane ta
 63. Daminan bana ba kamar ta bara ba, kwado ya fada ruwan zafi
 64. Damo sarkin hakuri
 65. Da na sani keya ce a baya akan barta
 66. Dattijo baka kukan aski
 67. Daudar gora kowa zai sha ta
 68. Dinyar makaho ta nuna a hununsa
 69. Dillalin wada shi ya san kudin jariri
 70. Dogayen kunnuwa ba zasu sa ji ba
 71. Dogaro ga Allah jari ne
 72. Dole ne a ce wa mijin Iya Baba
 73. Dole ne zuwa biki da muni
 74. Dole sai an yi kaciya ga yaro
 75. Dole ne a bambanta dan duma da na kabewa
 76. Dole ne a bambanta aya da tsakuwa
 77. Dole ne a bambanta zare da abawa
 78. Dole kare ya mutu da haushin kura
 79. Dole gyada ta yi mai, in ta ki ta sha matsa
 80. Domin munafuki gari bai kin wayewa
 81. Don ganin hadari ba a zubda ruwan buta ba
 82. Don mugun nufi ba a dinkin lifidi
 83. Dokin mai baki ya fi gudu
 84. Dokin da na san i ba ya yaki
 85. Don hannun ka ya rube, ba ka yankewa ka yar
 86. Don kai ake hula, har kunne ya samu
 87. Duniya ba gaskiya, barawo ya rasa shaida
 88. Duniya budurwar wawa
 89. Duniya mai ido tsakar ka
 90. Duniya zaman ‘yan marina, kowa da inda ya fuskanta.
 91. Duniya mace da ciki, ba a san abinda zata haifa ba.
 92. Duniya juyi-juyi, kwado ya fada ruwan zafi
 93. Duniya juyi-juyi mai doki ya koma kuturi
 94. Duniya rawar ‘yan mata, na gaba ya koma baya
 95. Duniya kamun kifi, kowa ya kamo ya sa a goransa
 96. Duniya ba lafiya, tunda ba’a kashe mutuwa ba
 97. Duniya rumfar kara ba ta da wuyar rushewa
 98. Duniya gidan kashe ahu wanda ya kasha taro yay i barna/zari
 99. Durkusa wa wada ai ba gajiyawa ba ne.
 100. Duddugar kaya, ta fi kayar zafi
 101. Dutsen tsakiyar ruwa bai san ana rana ba
 102. Duk abin da ya ci doma ba zai bar awai ba
 103. Duk abin da aka jefa sama, kasa zai fado
 104. Duk abin da mutum ya shuka shi zai girba
 105. Duk abinda ya taba hanci, idanu ruwa suke
 106. Duk abin da lauje ya yanka, ciyawa ne
 107. Duk abinda ka gani a gidan sarki, ya na kasuwa
 108. Duk dan da ya hana uwarsa bacci, shi ma ba zai runtsa ba
 109. Duk daya ne, makaho yayi dare
 110. Duk daya ne, mara sallah ya je gidan bamaguje
 111. Duk dadin madi, zuma ta fi shi
 112. Duk dacin gaskiya shan ta ya fi shan kwaryar zuma
 113. Duk dukiyar ka, kiyayi mai nema
 114. Duk in da wani ya tafi tsirara da sanin mai riga ne
 115. Duk inda ka ga hanya, in ba gari ya nufa ba, rafi ne
 116. Duk kyan takalmi, sai an taka shi
 117. Duk mai nashi ba ya kunyata
 118. Duk mai jinkiri, baya nasara
 119. Duk mai musun damina, ya saurari kukan kwadi
 120. Duk mai rai mamaci ne
 121. Duk nama ne, jakin maguzawa ya mutu
 122. Duk tashin tsuntsu, sai sama ta ga bayan shi
 123. Duk wanda bai ji bari ba, ya ji hoho
 124. Duk wanda yaki ji, ba zai ki gani ba
 125. Duk wanda ya ce wutar kara ta kwana, shi ya kwana bai runtsa ba.
 126. Duk wanda ya ga zara, zai ga wata
 127. Duk wanda ya raina tsayuwar wata, ya hau ya gyara
 128. Duk wanda yace bayanka na da kashi ka taba goya shi
 129. Duk wanda yace zai hadiye gatari, a rike masa kota
 130. Duk wanda yayi zagi a kasuwa, ya san da wanda yake yi
 131. Duk wanda ya tuna bara, bai ji dadin bana ba
 132. Duk wanda yake son rawa, ya koya wa dansa kida
 133. Duk wanda aka gani da tabarma, yana neman wurin shinfida ne
 134. Duk wanda ya ji haushin duniya, ya gaji da ita ne
 135. Duk wanda hannunsa ya kirga riba, wataran zai kirga faduwa
 136. Duk wanda ya daure kura, ya san yadda zai kwance ta
 137. Duk wanda ya zubar mini da tsamiya, zan zubar masa da nononsa
 138. Duk wanda yayi maka kan kara, kayi mashi na itace
 139. Duk wanda yayi noma ya huta da awo
 140. Duk wanda ya so musanya, ya raina nashi ne
 141. Duk yadda ake yi da jaki, sai ya ci kara
 142. Duk zafin tukunya dole a sauke
 143. Duk zurfin ruwa akwai yashi a ciki

F

 1. Fada wurin ban kashi
 2. Faduwa ta zo daidai da zama
 3. Fadan da ya fi karfinka, maida shi wasa
 4. Fadi alheri ko ka yi shiru
 5. Fata na gari lamiri ne
 6. Fatara mai tada tsohon bashi
 7. Farar aniya laya ce, wanda ya zo da bakaya sanya abinsa
 8. Farin wata raka wawa
 9. Farin wata sha kallo
 10. Farin cikin barawo ya sami kofa a bude
 11. Fawa ta gagari ‘yan fawa, balle ‘yan fince
 12. Filin sukuwar doki ba  a gurguwar jaka bane
 13. Fushin masoyi ya fi dariyar makiyi
 14. Furar jiya ce ta kasa tsami

G

 1. Gaba damisa baya sayaki
 2. Gaba da gabanta, aljani ya taka wuta
 3. Gaba ta kai ni gobarar titi
 4. Ga doki har doki, amma kofaton na sakaina ne
 5. Ga fili ga mai doki
 6. Ga kanya ta nuna amma biri ya makance
 7. Ga koshi ga kwanan yunwa
 8. Ga maciji ba a nuna ja
 9. Ga mari ka tsinka jaka?
 10. Gado ba bakon tsirara ba ne
 11. Gadar zare rashin sani ke sa a bita
 12. Gadon Ali sai fanna, ramin kura sai ‘ya’yanta
 13. Gafiya tsira da na babinki
 14. Gane min hanya, makaho ya so tseg
 15. Gangara maganin makiyi
 16. Gangan dutse maratayin zare
 17. Gani ya kori ji, yadda koko ya fi kunun zaki
 18. Ga ni ga Allah barawo a hannun mata
 19. Gani da ido maganin tambaya
 20. Gani ga wane ya ishi wane tsoron Allah
 21. Ganin gidan kansa kare ya zagi kura
 22. Gani ai ba ci ba
 23. Ganin zumar wani, kada ta sa ka zubar da madacinka
 24. Ganyen doka daya ya fi na dorowa dari
 25. Garin banza a farau farau din banza yake karewa
 26. Garin neman kiba an sami rama
 27. Garin gudun targade an sami karaya
 28. Garkuwa mai tare harbi
 29. Gaskiya daci gare ta
 30. Gaskiya matakin nasara.
 31. Gaskiya ta fi tafin hannu cike da zuma
 32. Gaskiya tafi kwabo
 33. Gaskiya dokin karfe, duk wanda ya hau ba zai yi nadama ba
 34. Gatari da wuta mai wuyan rataya
 35. Gero ya saba da ruwa tun ba a surfa ba
 36. Gidan maki-gudu sai da kara kan nuna
 37. Gida da yawa maganin gobara
 38. Gida biyu maganin gobara
 39. Gindin kura ya saba da raba
 40. Girma aka fi dauro, ba tsaba ba
 41. Girman kai rawanin tsiya
 42. Girma da arziki shi ya sa ake jan sa da abawa
 43. Girma da arziki ke jan rakumi ba akala ba
 44. Girma ya fadi, rakumi ya shanye ruwan kaza
 45. Giwa ta fadi kowa ya yanka rabon sa
 46. Gobara daga kogi maganin ta Allah
 47. Guntun gatarinka yafi sari ka bani
 48. Gudu samun sarari
 49. Guga ba ki tsoron rami
 50. Gurgu ya kama barewa mai kafa ya kasa
 51. Gurnanin damisa Karen gida ke tsoro
 52. Guda ba a yin ta da yare
 53. Gwani ba ka arziki sai suna
 54. Gwanin wani wawan wani
 55. Gwandar dawa, ga ruwa ga zaki
 56. Gwamma kwado da gaya
 57. Gwamma barnar ruwa da na wuta
 58. Gwano baya jin warin jikinsa
 59. Gyaran fuska ya fi gyaran gona
 60. Gyara kayanka ba zai zamo sauke mu raba ba

H

 1. Habaicin kura na mai akuya ne
 2. Hatsari ne abota da wawa
 3. Hadarin sama maganin mai kabido
 4. Hadin kai ya fi hadin baki
 5. Hadin kai shi ne karfi
 6. Haihuwar guzuma, uwa kwance, da kwance
 7. Hakorin hatsin tukunya, bas hi da wuyar karewa
 8. Hakuri maganin zaman duniya
 9. Hakuri jarin mai shi
 10. Haka da nade-nade, dan wake ya ga tubani
 11. Hakorin dariya shi ke cizo
 12. Hali zanen dutse, ba mai shafewa
 13. Hali ya rigaya mai horo
 14. Halin mutum sai Allah
 15. Halin mutum jarinsa
 16. Hanci bai san dandanon gishiri ba
 17. Hankaka kowa ya ga bakin ki, zai ga farin ki
 18. Hankaka mai da dan wani naki
 19. Hankali mudu auna shi ake yi
 20. Hange baya kawo nesa kusa
 21. Hanya ta fi gata
 22. Hanyar ruwa gangare
 23. Hanya mai hada zumuntar dole
 24. Hana wahala sai Allah
 25. Hannu da yawa maganin kazamar miya
 26. Hannu daya ba ya daukan jinka
 27. Hannun wani bai yi wa wani tagumi
 28. Hannun Bambara ya fi na dodon gona
 29. Hangen kitse ake wa rogo
 30. Hangen dala ba shiga birni ba ne
 31. Hanyar lafiya a bi ta da shekara
 32. Hankali ya fi wayo
 33. Hantsi ba hatsi hatsari
 34. Harbi gad an jaki gado
 35. Hassada ga mai rabo taki ne
 36. Hasken wata baya dai-dai da na rana
 37. Hausa ai ba dabo ba ce harshe ne
 38. Hauka dangi-dangi, kowa da irin nasa
 39. Hauka ja, hular dara ba tuntu
 40. Haushin kare, ba ya hana kura shiga gari
 41. Hayaki mai fidda na kogo
 42. Hayaki ba ya boyewa ko da a gidan marowaci
 43. Hikima kashin kwance, wanda bai iya ba, bata jikinsa
 44. Horo ba kisa ba, gyaran hali ne.

I

 1. Icen taba, Allah na ruwa tana bushewa
 2. Idan kura na maganin zawo ta yi wa kanta
 3. Idan aka bi salsala, jinin kaska na saniya ne
 4. Idan aski ya zo gaban goshi ya fi zafi
 5. Idan basira ta kare wa kare, sai ya daina haushi ya koma tunkuyi
 6. Idan balbela ta biya, zabuwa ta je da zanen ta
 7. Ido ba mudu ba, amma ya san kima
 8. Idan bori gaskiya ne, a fada rijiya
 9. Idan da alkawari ruwa ba zai ci gwani ba
 10. Idan da kwadayi da wulakanci
 11. Idan da rai da rabo
 12. Idan dajarar kaza ta fadi, har kwan da ke cikinta
 13. Idan hankali ya bata, hankali ke gane ta
 14. Idan ido ya mutu kwalli baya tada su
 15. Idan kai na da tsoka, kowa ya taba ya ji
 16. Idan kare na sunsunar takalmi, zai dauka ne
 17. Idan ka ga godiya da sirdi, wani ta kayar
 18. Idan ka ga baki da jini, na mai gardama ne
 19. Idan kunne ya ji, gangan jiki ya tsira
 20. Idan mafadin Magana wawa ne, mai ji ba zai zamo wawa ba
 21. Idan makaho ya rasa ido, sai ya ce yana wari
 22. Idan maciji ya sha wuya, in an yi walkiya, sai ya kai sara
 23. Idan mutum ya je gari, ya ga kowa da jela, shima ya nema ya sa
 24. Idan wani ya ki ka da wuni wani zai so ka da kwana
 25. Ido wa ka raina? Wanda na ke gani kullum
 26. Idan wukarka na da kyau, ba za ka gwada a jikinka ba
 27. Idan yaro makaho ne, babba mai jagora ne
 28. Idon da ya ga sarki ba ya tsoron galadima
 29. Ikon Allah, na zaune ya fadi
 30. Ikon Allah sai kallo
 31. Ilimi garkuwan dan adam
 32. Ilimi gishirin zaman duniya
 33. Ilimi mai yaye jahilci da duhun kai
 34. In Allah Ya taimake ka, ka taimaki na baya gare ka
 35. In Allah Ya ba ka ka gode sai ya kara maka
 36. In an gaji ko a rana a huta
 37. In an bi ta barawo, a bi ta ma bi sawu
 38. In an bugi kura a ka, an kara ma ta karfi ne
 39. In an ciza sai a hura
 40. In ana dara, fidda uwa ake
 41. In ana ta kai ba a ta kaya
 42. In ana fada ba a duban rauni
 43. In ana son ka da laifi, ko ruwa ka ashiga sai a ce ka tada kura
 44. In ajali ya kira ko ba ciwo sai an je
 45. In ba karamabani ba, me ya kai doki mahauta?
 46. In ba rami me ya kawo maganan rami?
 47. In ba ki da gashin wance, me ya sa zaki yi kitson wance?
 48. In ba ruwanka cikin Magana, ka bi ta da shiru
 49. In baka shan fura, bari damun ta
 50. In baka isa ba ka isa da kanka
 51. In baka son mutum, baka hana shi dariya
 52. In baka san gari ba, saurari daka
 53. In ba ka da kudi, me ya sa za ka kira mai alewa?
 54. In ba ka iya kyauta ba, ka bai wa mai baka
 55. In bera na da sata daddawa da wari
 56. In da duniya tana da gaskiya da ba a bar mazari tsirara ba
 57. In dambu ya yi yawa ba ya jin mai
 58. In duka yayi yawa, na ka ake tarewa
 59. In duniya ta ki mutum, sai kunkuru ya tsere wa karensa
 60. In ganga ta cika zaki, ta kusa fashewa ne
 61. In gemun dan uwanka ya kama da wuta, shafa wa naka ruwa
 62. In gemun dan uwanka ya kama da wuta, ka taimaka a kashe
 63. In gara ta ci tukunya, mai gora ya rataye abinsa
 64. Ingarma ke gudu, kura sai wahala
 65. In ka bi daga –daga na kurya kan sha kashi
 66. In ka ji gora na rawa ba cikakkiya ba ce
 67. In ka ji gangami da labari
 68. In ka iya ruwa ba ka iya laka ba
 69. In ka iya ruwa ba ka iya yashi ba
 70. In ka na son sauri aiki yaro inda yake so
 71. In ka na cin kasa, kiyayi ta shuri
 72. In ka ga kurma na gudu, ka bi shi, ganau ne
 73. In ka ga dan kunne a rumbu, idan ba a shiga ba an leko
 74. In ka ga kura da rana, me ya sa za ka bari ta cije ka?
 75. In ka ga ruwa a ido, daga ka yake
 76. In ka ga kuda daga dauda ta ke
 77. In ka ga ki gudu sa gudu bai zo ba
 78. In ka ga maciji a mike, ba za ka ce zai yi sara ba
 79. In ka san wata, baka san wata ba
 80. In ka sha rana wani zai sha inuwarka
 81. In kasuwa ta ki, sai ka kasa barkono a ce ba yaji
 82. In kunne ya ji gangan jiki ya tsira
 83. In kana da kyau ka kara da wanka
 84. In kida ya sauya, sai rawa ya sauya
 85. In kwana ya  kare, ba tsimi ba dabara
 86. In man shanu ya lalace, sai a toya yaki kanshi
 87. In maye ya manta, uwar diya ba za ta manta ba
 88. In maciji ya sari mutum, in ya ga tsumma sai ya gudu
 89. In mai gado ya zo mai tabarma sai ya nade
 90. In makaho ya ce bai ganin rana, ba ya sauya komai
 91. In makaho y ace a yi wasan jifa, ya taka dutse ne
 92. In nayi maka rana, kada ka yi min dare
 93. In nono na da dadi, bumba na da gardi
 94. In rakumi da girma, kayansa ma da yawa
 95. In ruwa yayi ruwa, kunkuru ma wurin fakewa zai nema
 96. In rana ta fito, tafin hannu baya kare ta
 97. In sayar da akuya, ta zo tana ci mini danga?
 98. In ta yi ruwa rijiya, in ta ki masai
 99. In tukunya ta tafasa, ba ta barin gefe
 100. In ungulu ta biya bukata, zabuwa ta je da doronta
 101. In wata ya yi fari a kasa zai nuna
 102. In za ka gina ramin mugunta, gina shi gajere
 103. In za ka yi Magana da kurma, sai ka zungure shi
 104. In zamani ya dinka riga, ta ishi kowa
 105. Ina akuya za ta da kayan taiki?
 106. Ina amfanin badi ba rai?
 107. Ina ruwan kifi da kaska?
 108. Ina ruwan kallo da gajiya?
 109.  “Ina ji a jika” kabiyar mahauci
 110. Ina tukunyar damo, ina na guza? Duk daya ne
 111. Inda ba kasa, nan ake gardamar kokuwa
 112. Inda biri ya san ashana, da ya kona gari
 113. Inda aka san darajar goro, ake masa tanadin ganye
 114. Inda baki ya karkata, nan miyau kan zuba
 115. Inda ba ci ba sha, ruwa magani ne
 116. Inda badon wari ba, tafarnuwa ta fi zinari daraja
 117. Inda fata tafi taushi akan bi ta da jima
 118. Inuwar giginya, na nesa ke shan sanyinta
 119. Inuwar bagaruwa ga sanyi ga kaya
 120. Iska na wahalar da mai kayan kara
 121. Itatuwa abincin giwa in ta ki ta kwana da yunwa
 122. Iya rai iya buri
 123. Iya rai iya gani
 124. Iya ruwa fid da kai, mai fid da kanshi sai gwani
 125. Iya yi ci-rani ba miji

J

 1. Ja da baya ga rago ba tsoro bane shirin fada ne
 2. Ja ya fadi, ja ya dauka
 3. Ja maganin mushen doki
 4. Jahilci ya fi duhun dare
 5. Jahilci ya fi hauka wuyar warkewa
 6. Ji da kai kamar bulalar maye
 7. Jifan mahaukaci yakan fada wa mai tsautsayi
 8. Jikan jatau, bakin mutum ya ga fari
 9. “jiki magayi” shan tabar mai koyo
 10. Jita-jita karatun bamaguje
 11. Jimina ko ya yi cara, ba za a kirashi zakara ba
 12. “jiya ba yau ba” tsohuwa ta ga tatakwashi
 13. Jinkirin tuba karamin kafirci ne
 14. Jin labarin gwani, ya fi ganin raggo
 15. Jin kunyar maras kunya asara ne
 16. Jumma’a da za tayi kyau tun daga labara ake gane ta
 17. Jure fari sai tofa
 18. Juyi tara sai wake

K

 1. Ka ki ni dubu su so ni
 2. Ka so makiyinka, sai ya rasa mafita
 3. Ka bar ganin griman kuka, bagaruwa Ita ce babba
 4. Ka da zomo biyu su gaza miya
 5. Ka da cibi ya zama kari
 6. Ka da reshe ya juye da mujiya
 7. Ka da allura ta tono garma
 8. Kada ka sake ruwa ya cika a wankin kalwa
 9. Ka da ka yi saka da mugun zare
 10. Ka da ka riga malam masallaci
 11. Ka da mage ba yanka ba
 12. Ka da hangen hadari ya sa a yi wanka da kashi
 13. Ka da ka zama kanywa uwar gami
 14. Ka da kunkuru yayi wa bushiya kafa
 15. Kato da gora maganin zauna gari banza
 16. “kamar da kasa” inji mai ciwon ido
 17. Kanari mai dadin kuka, duk wanda ya ji sai ya waiga
 18. Kadangaren bakin tulu a kashe ki a fasa tulu, a bar ki, ki bata ruwa
 19. Kaikayi koma kan mashekiya
 20. Ka kiyayi furfura, ko da ta arne ce
 21. Kainuwa dashen Allah, ba dashen mutane ba
 22. Kafa baya zuwa inda zuciya bata so
 23. Kafar ungulu mai bata miya
 24. Kafin ka ga biri, biri ya gan ka
 25. Karfen aska sai zababbe
 26. Karambanin akuya gaida kura
 27. Karen bana shi ke maganin zomon bana
 28. Karfe daya ba ya amo
 29. Karkatacciyar kuka mai dadin hawa
 30. Da Kai da kaya, duk mallakan wuya ne
 31. Kama da wane ba ta wane
 32. Kara da kiyashi daukar maras sani
 33. Karen da ba ka ciyar da shi bai jin kiranka
 34. Karya fure take ba ta ya’ya
 35. Karatu farkonki madaci karshenki zuma
 36. Kagara gari ya waye ke kawo tsawon dare
 37. Karshen lalacewa, namiji da guda
 38. Kallo ya koma sama, shaho ya dauki giwa
 39. Kare yayi haushi hakoran shi sun zube
 40. Kare mai zalama, a ba shi kan giwa
 41. Kayan nama ba zai kasha kuraba
 42. Karambanin bako a kori barawo ya kai gudummawa
 43. Karamin sani kukumi ne
 44. Karamar zuci, gwauro da turaka
 45. Karamin goro ya fi babban dutse
 46. Kasuwa a kai miki dole
 47. Kashin kare ba ya taki
 48. Kasha baya samar da jini sai tsoka
 49. Kazar kwanci me kwakwazo
 50. Kaza tana taka ‘ya’yanta badon ki ba, sai don suyi kwari
 51. Kaza mai ‘ya’ya ke tsoron shirwa
 52. Kaza ba ta da nono, Allah ke ciyar da ‘ya’yanta
 53. Kere na yawo zabo na yawo watarana a hadu
 54. Koshin wake na ruwa ne
 55. Karshen alewa kasa ne
 56. Karya linzamin shaidan
 57. Kidan jajibiri  baya tada hankalin kare
 58. Kitse mugun nama bai nuna ba ya kashe wuta
 59. Kifi na ganin ka mai jar koma
 60. Kifin fadama ba ya gasa da na gulbi
 61. Kishi kumallon mata, in ya motsa sai an haras
 62. Kibiyar aljali sulke ba ya tsare ta
 63. Kiwon kai ya fi kiwon dabba
 64. Ko a kwara da tsibiri
 65. Ko biri ya karye zai hau rumbu
 66. Ko ba a gwada ba linzamii ya fi karfin bakin kaza
 67. Ko ba a yi don mai gayya ba a yi don mai gona
 68. Ko da girgiza kurna ta fi magariya ‘ya’ya
 69. Ko da kudinka, sai da rabonka
 70. Ko da washi gatari ba zai yi wa dutse komai ba
 71. Ko shamuwa ta sha ruwa ba za ta zama shirwa ba
 72. Ko gobe ruwa na maganin dauda
 73. Ko yaro a goye, ya san kura
 74. Komai dadin karya, gaskiya ta fi ta
 75. Komai dadin kida shiru ya fi shi
 76. Komai dadin guda, ba a yi ma asara
 77. Komai daki ya samu albarkacin kofa ne
 78. Komai gudun barewa a hannun mai dawa zata kwana
 79. Komai hasken farin wata, dare abin tsoro ne
 80. Komai kankantar tsuntsu, ba za a ci shi da gashi ba
 81. Komai kasaitan agola ba zai yi gado ba
 82. Komai na duniya kararre ne, ban da ikon Allah
 83. Komai nisan gari akwai wani a gabansa
 84. Komai nisan gari, masoyi baya ganin nisan sa
 85. Komai nisan jifa, kasa zai fado
 86. Komai nisa dare gari zai waye
 87. Komai saurin ungwarzoma ta bari a haihu
 88. Komai wuya da mai  jin dadi
 89. Komai iya surfe ba za ‘a daka dutse ba
 90. Komai lalacewar masa, ta fi kashin shanu
 91. Komai laushin gari ba zai hana a tankade ba
 92. Komai ramar giwa ta fi Kwando goma
 93. Komai yawan kitse baya huda hanji
 94. Koma ya ji ban da barkono a ido
 95. Komai ya yi farko zai yi karshe, ban dan Idon Allah
 96. Komai yayi fari yana da nagarta, ban da kurkunu
 97. Komai yayi zafi, zai yi sanyi
 98. Komai ya sami shamuwa, watan bakwai ne ya ja masa
 99. Komai zaka fadi, fadi gaskiya komai ta ja maka ka biya
 100. Komai zafin abinda kake ci, wuta ta fi shi
 101. Komai zafin ruwa, yana kasha wutar kara
 102. Kowa da irin kiwon da ya karbe shi makwabcin mai akuya ya sayi kura
 103. Kowa da masoyinsa, jaki ya ga toka
 104. Kowa ya dogara ga Allah, kada ya ji tsoron mahassada
 105. Kowa ya bar gida, gida ya bar shi
 106. Kowa ya daka ta rawar wani, ya rasa turmin daka tasa
 107. Kowa ya daka ta bado, ruwa ya ci shi
 108. Kowa ya iya allonsa, ya wanke
 109. Kowa ya ci ladan kuturu dole ya yi mashi aski
 110. Kowa yayi hakuri za a yi da shi
 111. Kowa ya ci zomo ya ci gudu
 112. Kowa ya ce zai kona rumbunsa, ya san inda toka ke daraja
 113. Kowa ya debo da zafi bakin sa
 114. Kowa ya hadiye tabarya, ya kwana a tsaye
 115. Kowa ya raina gajere bai taka kunama ba
 116. Kowa ya sayi rariya ya san za ta zubda ruwa
 117. Kowa ya sha inuwar gemu baya makogwaro
 118. Kowa ya goya kare ya san yadda zai yi da bakin
 119. Kowa ya tuna bara bai ji dadin bana ba
 120. Kowa yayi kwalliya ya na son yabo
 121. Kowa ya kwana lafiya shi ya so
 122. Kowa ya ga gidanka ka ga nasa
 123. Kowa ya so uwa, ya so danta
 124. Kowa yayi da kyau, ya ga da kyau
 125. Kowa yayi fari  ya gama kyau
 126. Kowa ya hana ka dakin kwana, dole da safe ya gan ka
 127. Kowane mai rai ajizi ne
 128. Kowane kwarya da abokin burminta
 129. Kowane tsuntsu kukan gidansu yake yi
 130. Kowane gauta ja ne, sai dai bai ji rana ba
 131. Kowane bakin wuta da nashi hayaki
 132. Kosawa da arziki jahilci ne
 133. Kora da hali ya fi kora da sanda
 134. Kuturu ba bakon miki ba ne
 135. Kuda wajen kwadayi a kan mutu
 136. Kudi masu gidan rana
 137. Kudin cuta, na mai magani ne
 138. Kukan kurciya jawabi ne, mai hankali ke ganewa
 139. Kukan ciki ya bambanta da na gwaiwa
 140. Kulba na barna ana cewa jaba ne
 141. Kula da kaya ya fi ban cigiya
 142. Kuliya manta sabo
 143. Kunnen giwa ya fi karfin talla
 144. Kunne ya girmi kaka
 145. Kura bata san kudin akuya ba
 146. Kura da shan bugu gardi da kwashe kudi
 147. Kura, ga tsoro ga ban tsoro
 148. Kura kin cin naki kin ci na dangi
 149. Kura ta san gidan mai babban sanda
 150. Kushe da hasssada ba su hana bawa rabon sa
 151. Kushewar badi sai badi
 152. Kwai a baka ya fi kaza a akurki
 153. Kwace goruba a hannun kuturu ai ba wuya
 154. Kwaryar kira jure tarkace
 155. Kwarya ta bi kwarya, in tabi akushi ta fashe
 156. Kwarya dole ta fito ranar shika
 157. Kwado ke nan ba da cizon dan kowa
 158. Kwadayi, mabudin wahala
 159. Kyaun da, ya gaji ubansa
 160. Kyaun da, ya fi ubansa
 161. Kyaun tafiya, dawowa lafiya
 162. Kyanwa a garin wasu damisa ne
 163. Kyanwan lami ba kuka ba yakushi
 164. Kyaun kwado aci da yaji
 165. Kyauta ba ya hana arziki

L

 1. Labarin dare, a tambayi kura
 2. Labarin gizo ba ya wuce koki
 3. Labarin zuciya, a tambayi fuska
 4. Laraba ta bawa ranar samu
 5. Laifi ba shi da ubangiji
 6. Laifin wani ba ya shafar wani
 7. Laifi tudu ne, ka taka naka ka hangi na wani
 8. Lafiyar namiji gadon bayansa
 9. Lafiya uwar jiki, babu mai fushi da ke
 10. Laifin babba rowa, laifin yaro kwiya
 11. Laifin kura dubu, banda satan akuya
 12. Lallai, wata sabon gani ne
 13. Lokacin abu a yi shi
 14. Linzami da wuta maganin sangartaccen doki
 15. Linzami ya fi karfin bakin kaza

M

 1. Maciyinka ba ya ganin ramarka
 2. Mafarin hauka, tsirta yawu
 3. Madoki kusa maciji nesa
 4. Madugu uban tafiya ne
 5. Magana ba madogara, yin kwalli da tabarya
 6. Makaho na da ido amma ba na ganin gari ba
 7. Magana ba kaya ba ne, in ka yi sai a yi maka
 8. Maganar fari shi sarki kan kama
 9. Magana zarar bunu ce, in ta fita ba a mayarwa
 10. Magana baya fasa kasha, yakan bata zuciya
 11. Maganin biri, Karen maguzawa
 12. Magana ai jari ce
 13. Magori, wasa kanka da kanka
 14. Mai abin fada ba ya fada
 15. Mai arziki ko a kwara ya sai da ruwa
 16. Mai akuya ya bi dare, balle mai kura?
 17. Mai bunu, bay a zuwa gudummawar gobara
 18. Mai cinikin shan zuma, in reshe bai karye da shi ba, kwarya ta fashe masa
 19. Mai cininkin sara, shi ke sanin faduwar gatari
 20. Mai cinikin karya, yay i biyan gaskiya
 21. Mai cin dambu, ba a ce masa ga ruwa
 22. Mai daki shi ya san inda yake zuba
 23. Mai dan kwikwiyo shi ke da kare
 24. Mai dokan barci, ya bingire da gyangyadi
 25. Mai farautar kura, ba ya zuwa da kare
 26. Mai gyara ba ya barna
 27. Mai gudun gara ya fada zago
 28. Mai hali ba ya barin halinsa
 29. Mai hankali shi ke gane sawun gwauro a kasuwa
 30. Mai hankali shi ke bai wa kaza ruwa da damina
 31. Mai hankali shi ke kyautata wa bako
 32. Mai hankali ke gane furfurar tunkiya
 33. Mai ido daya ba zai yi nadama ba, sai ya ga makaho
 34. Mai ido da rami da wuri yake kuka
 35. Mai ido a ka ba a nuna mashi sama
 36. Mai kyauta ba ya rasawa
 37. Mai kyau moran kowa
 38. Mai kaza a aljihu, ba ya jimirin as
 39. Mai kaza a akurki ba ya jimirin as
 40. Mai kaya shi ke tsoron fashi
 41. Mai karambani shi ke biyan bashin kaka
 42. Mai laya kiyayi mai zamani
 43. Mai madi ke talla, mai zuma sai a same shi a saya
 44. Mai neman gada, in ya ga akuya ya huta
 45. Mai nema na tare da samu
 46. Mai roko surukin mai rowa
 47. Mai rai ba ya rasa motsi
 48. Mai raina kadan barawo ne
 49. Mai rabon ganin badi ko ana ha maza ha mata sai ya kai
 50. Mai rabon ganin badi ko ana ruwan masu, sai ya kai
 51. Mai rabon shan duka baya jin kwabo sai ya sha
 52. Mai rawar kai ba ya digirgire
 53. Mai rigar tsumma baya shiga gonar karangiya
 54. Mai son kuka, an jefe shi da kashin awaki
 55. Mai son dan tsuntsu shi ke bin sa da jifa
 56. Mai tarko baya ta da kara
 57. Mai takama da madi ya koma shan zuma
 58. Mai uwa a murhu, ba ya kwana da yunwa
 59. Mai uwa a murhu, ba ya cin tuwonsa gaya
 60. Mai waina da ruwa, balle ta samu mai?
 61. Mai zuciya ake gaya wa biki ba mai kudi ba
 62. Mai da ruwa rijiya ba laifi ba ne
 63. Masanin dare duhu ne
 64. Masu kumatu su ke da yawu
 65. Masha ruwa magirmi
 66. Matambayi ba ya bata
 67. Matar mutun kabarinsa
 68. Matar na tuba ba ta rasa miji
 69. Matar shige ba ta daraja
 70. Matan zamani ba tukwane ba, balle a kwankwasa a ji wanda ta fi kwari
 71. Mahakurci mawadaci
 72. Maras gaskiya ko cikin ruwa ya yi jibi
 73. Maras son jini ba zai je mahauta ba
 74. Maras kunya ke cin tuwon biki har ya kare
 75. Makaho bai san ana ganin sa ba, sai an zungure shi
 76. Maso ganin dare, ya bi kura
 77. Maso abinka ya fi ka dabara
 78. Maza gumban dutse ne
 79. Man kadanya ba zai zauna a tandu ba
 80. Me ya kai fura zani? In ba kazamiyar damu ba
 81. Me ya hada kifi da kaska?
 82.  “Me aka yi” an ga mahaukaciya ta shiga rawa
 83. “Me ake jira” gwari ya yi toshi
 84. Me iska za ta yi da kayan kara?
 85. Me na ci na ashan zanyi ramakon azumi?
 86. “Me zan ce” zanin aro ya kone?
 87. Me kuturu zai yi da zoben tsintuwa? Sai dai ya ba da cigiya
 88. Mu tafi a hankali, mu yi guzuri da katon sanda
 89. Muje mu gani, maganin mai karya
 90. “Muje zuwa” mahaukaci ya hau kura
 91. “Mulkin mallaka” biyan bashi da dan kishiya
 92. Munduwar wuya, ana son zarewa ana tsoron jin ciwo
 93. Mugu shi ya san kawancin mugu
 94. Muguwar miya ba ta karewa a tukunya
 95. Mugun dafi a bar wa macizai
 96. Mugunta fitsarin fako
 97. Mun gaji da kyau hali muke nema
 98. Munafunci dodo yakan ci mai shi
 99. “Muna wasa ne” gwari ya ba da magani an mutu
 100. Mummunan farko yakan yi kyakkyawan karshe
 101. Mutunci madara ne, idan ya zube ba a kwashewa
 102. Mutunci ya fi kudi
 103. Mutuwa rigar kowa
 104. Mutuwar yawa kaka
 105. Mutuwar uwar adashe ba karshen adashe ba ne
 106. Mutuwar zuciya gai da makiyi da safe
 107. Mutuwa karar kwana, fashi barnar aiki
 108. Mushen gizaka, ta mutu amma ta na ba yara tsoro
 109. Na shiga ban dauka ba, ba ta fidda barawo

N

 1. Naka naka ne, ko ya ci namanka ba zai tauna kashinka ba
 2. Naci kamar kwarton kusa
 3. Naci ai damben kuturu ne
 4. Na taba ki da alheri, kishiya ta taba kishiya da bakin wuta
 5. Na ji dadi shi ne gari ban a saba ba
 6. Na gaban wuta shi ke jin duminta
 7. “na ga abinda ya ishe ni” in ji kishiyar mai mata tara
 8. Nagari na kowa mugu sai mai shi
 9. Namiji barkono, sai an dandana ake sanin yajinsa
 10. Naman sallah ko wanda ba shi da gida zai ci
 11. Nan gani nan bari farar tumfafiya
 12. Nasara na wajen Allah
 13. Na zaune gwanin kokuwa
 14. Na zaune bai ga gari ba
 15. “Na zo ke nan” shigar sojan Badakkare
 16. Noma tushen arziki
 17. Noma yanke talauci
 18. Noma na duke tsohon ciniki
 19. Nuna sani a kasuwar jahilai, wauta ne
 20. Nuna yatsa, ba shi ake kira nuni ba
 21. Nuni a cikin nishadi

R

 1. Ra’ayi kukan jaki ba a iya hanawa
 2. Ra’ayi riga, kowa da irin ta sa
 3. Rabon akuya tsari, farau-farau sai mai gata
 4. Rabon kwado baya hawa sama
 5. Rabo ajali ne
 6. Raba bawa da arziki sai Allah
 7. Raba da da mahaifi sai Allah
 8. Raba ni da cusa kai ba kwarjini
 9. Rai dangin goro ne, ya na son ruwa
 10. Raina kama ka ga gayya
 11. Raina da kuna, kaza ta yi shekan dari
 12. Raon Malam ga kitse, ga arha
 13. Rago aka sani da tunkuyi ba kare ba
 14. Rakumin dawa ba’a hawan shi ba a dora masa kaya
 15. Ramakon gayya tafi ta gayya zafi
 16. Ramin karya kurarre ne
 17. Ramin shuka ba zurfi gare ta ba
 18. Ran sarki ya dade, bay a hana shi mutuwa
 19. Rana mudun aiki ne
 20. Rana ba ta karya sai dai uwar diya ta ji kunya
 21. Ranar wanka ba a boyon cibi
 22. Ranar yanka ba a boye wuka
 23. Rashin hakuri shi ya sa ake me aka shuka?
 24. Rashin sani ya sa makaho taka sarki
 25. Rashin sani Karen gwauro ya kori bazawara
 26. Rashin hakurin ‘ya mace, ta haihu a gidan iyayenta
 27. Rashin sani ya fi dare duhu
 28. Rijiya ta ba da ruwa guga ya hana
 29. Rijiyar mai hassada, wawa ke shan ruwanta
 30. Rijiya gaba dubu, duk wanda ya gina ki ya bai wa Allah
 31. Rigakafi ya fi magani
 32. Rigen zuwa fada ba shi ne ganin sarki ba
 33. Rigen zuwa kasuwa ba shi ne riba ba
 34. Rimi adon gari
 35. Rikon mahaukaci sai sarki
 36. Roki maroki ka ga rokkakiyar rowa
 37. Rufin asirin mai loma, ka da a yi walkiya
 38. Runbun tunani bakin ciki ne yakan cika shi da tokar tunanin
 39. Rumfar kara ba ki boye hayaki
 40. Ruwa ba sa’an kwanda ba ne
 41. Ruwa ba ya tsami banza
 42. Ruwa da dorina da kada bako ke wanka cikinta
 43. Ruwan dare gama duniya
 44. Ruwa iya wuya maganin mara son wanka
 45. Ruwan tsami ba ya kauri
 46. Ruwa ya kare wa dan kada bai gama wanka ba
 47. Ruwa shuka ya kauda na sassabe
 48. Ruwan ido ba zai yi kwaben kasa ba
 49. Ruwan wuta mai jiran bacin rana
 50. Rufe ido ba makanta ba ne
 51. Rufin asiri sai Allah

S

 1. Sa’a wanda ta fi manyan kaya
 2. Sa’a ta fi sammako
 3. Sabo da yi, guda a gidan mutuwa
 4. Sabo da yi gawa da gatsine
 5. Sabo da kaza ba ya hana yanka ta
 6. Sabo da maza jari ne
 7. Sai an gwada akan san na kwarai
 8. Sai an huda kasa akan samu ruwa
 9. Sa kai, wanda ya fi bauta ciwo
 10. Sakaina gwanin iya ruwa
 11. Sai  hali ya yi daidai ake abota
 12. Sai an ji dadin gwanda ake tanadin irinta
 13. Sai bango ya tsage, kadangare ke samun wurin shiga
 14. Sai an sha wuya akan tuna Allah
 15. Sa rai da ci shi ke kawo jin yunwa
 16. Sarfa gandun baiwa
 17. Sarautar Allah, kare a bakin zomo
 18. Sara da sassaka, ba ya hana gamji tofo
 19. Sarki goma zamani goma
 20. Sarkin yawa ya fi sarkin karfi
 21. Sakin na hannu kama na guje kamun gafiyar baidu
 22. Sallah ta wuce ta bar wawa da bashi
 23. Sallah mai biki daya rana
 24. Samu ya fi iyawa
 25. Samun shiga, barawo da sallama
 26. Sama ta yiwa yaro nisa, sai dai ya tada kai ya yi kallo
 27. Sannu bata hana zuwa sai dai a dade ba a je ba
 28. Sannu ba ta maganin harbin kunama
 29. Sanin asali ya sa kare cin alli
 30. Sanin gaibu sai Allah
 31. Sanin asirin ciki sai hanji
 32. Saniya da shafa ake tatsarta
 33. Sana’a goma maganin gasa
 34. Sanin darajar toka, ke sa mutum kona rumbunsa
 35. Sandar girma ba a zunguri da ke sai nuni
 36. Sandar jifan kura da safe ake dauko ta
 37. Sandar da aka kori tsiya da ita ba a yarwa
 38. Sawun giwa ya take na rakumi
 39. Sauri ya haifi nawa
 40. Sau daya gyadar makaho ya kone, na biyu ya ci abinsa danye
 41. Saurin fushi shi ke kawo dana sani
 42. Sauki, ture zabo kwashe kwai
 43. Sauki baya hana riba
 44. Sata a gidan barawo rance ne
 45. Sata hali ne, mai yinta komai wadata sai ya yi
 46. Sayen na gari mai da kudi gida
 47. So duka so ne amma son kai ya fi
 48. So mai  hana ganin laifi
 49. Son Allah ya fi taron dangi
 50. Son kira, kamar bazarawa
 51. Son kowa, kin wanda ya rasa
 52. Son jiki kamar gyambo
 53. Son jiki kamar mage
 54. Son maso wani cuta ne
 55. Son zuciya bacin zuciya
 56. Soyayya gamon jini ne
 57. Soyayya ta fi kudi
 58. Shari’a kamar kayan aras take, ba ta son garaje
 59. Sharia’a sabanin hankali
 60. Shashanci yin gaba da bako
 61. Shinfidar fuska ta fi shimfidar tabarma
 62. Shan ruwa ba ya hana mutuwa
 63. Shakuwa, mai neman rai
 64. Shagwaba, tarwada da kukan kishin ruwa
 65. Shegen kaya, dare akan bi da shi
 66. Shiru ka ke ji, an aiki bawa garin su
 67. Shiru ka ke ji, mai kalangu ya fada rijiya
 68. Shure-shure ba ya hana mutuwa
 69. Shiga da fita ba ya yi wa azure komai
 70. Shirin zaune ya fi na tsaye
 71. Suna linzami ne, mai shi yake bi

T

 1. Taba ta bambanta da garin goro
 2. Tabarmar kunya, da hauka ake nade ta
 3. Ta faru ta kare, an yi wa mai dami daya sata
 4. Ta faru ta kare, an bai wa mayya karbar gaisuwan mutuwa
 5. Ta faru ta kare zanin aro ya kone
 6. Tafiya da gwani mai dadi, idan gwanin bai lalace ba
 7. Tafiya mabudin ilimi
 8. Tafiya sannu kwana nesa
 9. Tallar turmi ba a sayar ba sai kaya
 10. Ta Malam ba ta wuce amin
 11. Tambarin talaka cikinsa
 12. Tauraruwa mai wutsiya ganinki ba alheri ba
 13. Takalma lafiyar kafafu
 14. Takalmin kaza, mutu ka raba
 15. Takanda ai ba kasha ba ne
 16. Takaici mai sa babba kuka
 17. Tashin hankali cire wando ta ka
 18. Tasha ba ta haihuwa sai yaye
 19. Ta yaro kayu take ba ta karko
 20. Tun daga gida, damara ya kwance
 21. Tulu shi ke yawo, randa na zaune
 22. Tun ran gini ran zane
 23. Tunani mai sa amarya kuka
 24. Tuntuben kashi, idan ba a ji rauni ba rayuwa ta baci
 25. Tuntuben harshe, ya fi tuntuben kafa zafi
 26. Tururuwa bata gudun abin kunya
 27. Turmin tsakar gida sha lugude
 28. Tsabta cikon addini ne
 29. Tsakanin Dan Adam da kudi
 30. Tsintacciyar mage bata mage
 31. Tsintsiya madaurin ki daya
 32. Tsautsayin takaba, auren majinyaciya
 33. Tsalle daya shi ke jefa mutun rijiya
 34. Tsare gida mutuncin dandi
 35. Tsoro na daji, kunya na gida
 36. Tsokanar fada ne an cewa gwauro yaya iyali?
 37. Tsugune bata kare ba, an sayar da kare an sayi biri
 38. Tsakuwa a ruwa sai gwani
 39. Tsuntsun da ya kira ruwa, shi ruwa kan doka
 40. Tsumagiyar kan hanya, fyadi yaro, fyadi baba
 41. Tsuntsu mai wayo a wuya ake kama shi
 42. “To wanka na ke”, mahaukaci ya fada rijiya
 43. Tuwon kasa ba zai yi maganin yunwa ba
 44. Tuwon tulu mai wuyan kwashewa
 45. Tuwon kasa na kare ne, tuwon nama sai kura
 46. Tuwon girman miyan sa nama
 47. Turbar sama sai tsuntsu

U

 1. Ungulu ba kazar kowa ba ce, don ba a saka ta a akurki
 2. Ungulu ta koma gidanta na tsamiya
 3. Uwa ta fi uba, ko da uban sarki ne
 4. Uwar raggo ake wa barka
 5. Uwargida sarautar mata

W

 1. Wata sabon gani
 2. Wanda bai ji kunyar hawan jaki ba, ba zai ji kunyar kayar da shi ba
 3. Wanda bai ci arzikin wani ba sai ya mutu matsiyaci
 4. Wanda bai sami tarbiya a gida ba duniya za ta koya mashi
 5. Wanda bai yi sharan masallaci ba, ya yi na kasuwa
 6. Wanda kunama ya harba, in ya ga kyankyaso sai tsalle
 7. Wanda rakuminsa ya bata ko akurki sai ya leka
 8. Wanda ruwa ya ci ko takobi aka bas hi zai kama
 9. Wanda ya yi nisa ba ya jin kira
 10. Wanda ya jira kahon kare ya makara
 11. Wanda ya kai ya komo, shi ke sai da ruwa a kogi
 12. Wanda ya ci zomo, dole ya yi aman-gashi
 13. Wanda ya ci zomo, ya ci gudu
 14. Wanda ya san matsalar abinci, shi ke tanadin hatsi
 15. Wanda ya ki neman ilimi, jahilci zai kashe shi
 16. Wanda ya riga ka barci, zai riga ka tashi
 17. Wanda ya ki shan ruwan kwano, ba zai shiga rijiya ya sha ba
 18. Wanda ya saba zama a murhu, wataran zai kone
 19. Wanda ya yi hakuri da kunun maraice, yakan ga tuwon yamma
 20. Wanda ke inuwa bai san wani na rana ba
 21. Wanda ya daure kura shi ya san yadda zai kwance ta
 22. Wandon karfe, kowa ya sa ya kwana a tsaye
 23. Wanka da gari baya maganin yunwa
 24. “Wani abu haka”, wai gwanin rawa ya fadi
 25. Wani ma ya yi rawa balled makadi?
 26. Wani hani ga Allah baiwa ne
 27. Wani kaya sai amale, jaki ba zai iya ba
 28. Wani irin dare ne jemage bai gani ba?
 29. Wani tsuntsun na gudun ruwa, agwagwa a ciki ta ke kwana
 30. Wanzami ba ya son jarfa
 31. Waka bakin mai ita ta fi dadi
 32. Wake daya mai bata gari
 33. Wake ya nuna damo  ya makance
 34. Wai kwana nawa ne? maye yayi amariya
 35. Waiwaye adon tafiya
 36. Wargi wuri yakan samu
 37. Wawa shike rena mafari
 38. Wayo ya san na ki
 39. Wayon aci ne aka kori kare daga gindin dinya
 40. Wukar fiddar giwa ba kaifi gareta ba sai girma
 41. Wuyar noma kunyar fari
 42. Wutsiyar rakumi ta yi nesa da kasa
 43. Wuni da Malami ya fi shekara da jahili
 44. Wuya mai sa a kwana bayan suruka

Y

 1. Yaba kyauta tukwuici
 2. Yabon gwani ya zama dole ko da makiyi ba ya so
 3. ‘Yan mata adon gari
 4. Yara manyan gobe
 5. Yaro tsaya matsayin ka inka ki ka gane kuren ka
 6. Yaro ko yana wasa da kare ya kiyayi damisa
 7. Yaro bai san wuta ba sai ya taka
 8. Yaro da gari abokin tafiyar manya
 9. Yaro man kaza, in ya ji rana sai ya narke
 10. Yaro da rarrafe kan tashi
 11. Yaro wutar kara ne sai da kulawa
 12. Yaro a goye bai san nisan tafiya ba
 13. Yaro ya san kura, da ganin birni ya san ya fi garinsu
 14. Yaro bata hankalin dare ka yi suna
 15. Ya kamata kwalliya ta biya kudin sabulu
 16. Yau da gobe sai Allah
 17. Yau gareka gobe ga wani
 18. Yau fari gobe baki birgiman hankaka
 19. Yautai mugun tsuntsu
 20. Yawan shekaru ba shine wayo ba
 21. Yawa mai sa masu zare jan dutse
 22. Yawan mutune sune kasuwa, ba tarin rumfuna ba
 23. Yawan gaisuwa ya fi yawan fada
 24. Yawon dare bana dan akuya ba ne
 25. Yawon duniya shigar zungurun kadangare
 26. “Yaya na iya da raina”, mummuna ya ga matar aure
 27. ‘Ya’an marke kun nuna kun waste
 28. “Yay azan yi da abin da ya gagari wuta” in ji kishiyar konanna
 29. Yi nayi, bari na bari, shine aure
 30. Yi na yi, bari na bari, shine biyayya

Z

 1. Zafin nema ba ya kawo samu
 2. Zancen banza Magana ba iko
 3. Zancen banza, zakara ya taka wuka
 4. Zance da dan gari ilimi ne
 5. Zakaran da Allah ya nufa da cara, ana muzuru ana shaho sai ya yi
 6. Zakaran ka rakumin ka
 7. Zakara mai neman suna, bada kwaya ka ci tsakuwa
 8. Zakara a rataye ba ya cara
 9. Zalama, a ci kasuwa da kai ka koma kale
 10. Zalbe mai cinikin kasada
 11. Zaman duniya hakuri, makiya su fi masoya
 12. Zaman lafiya ya fi zama dan Sarki
 13. Zama da munafuki sai dole
 14. Zama wuri daya tsautsayi, inji kifi
 15. Zama da madaukin kanwa shi ke kawo farin kai
 16. Zato zunubi ko da ya zamo gaskiya
 17. Zarton yankan dutse ba a masa washi
 18. Zo mu zauna zo mu saba ne
 19. Zo mu ci tuwo yafi tuwon dadi
 20. Zomon daji shi ya san hanyar tserewa kare
 21. Zomo ba ya fushi da makashin sa sai maratayin sa
 22. Zomo ba ya kamuwa daga zaune
 23. Zumunta a kafa take
 24. Zuciya mai sa dana sani
 25. Zuciya ke gani, ba ido ba
 26. Zuciyar mutun birnin sa
 27. Zuwa da wuri, ya fi zuwa da wuri-wuri.

What do you think of these 1000 Karin Magana? Do you have an addition to make or a correction? Tell us in the comments section.

You May Also Like…

No Results Found

The page you requested could not be found. Try refining your search, or use the navigation above to locate the post.

0 Comments

Leave a Reply

Subscribe To Our Newsletter

Join our mailing list to receive the latest news and updates from our team.

You have Successfully Subscribed!

Pin It on Pinterest